Sakatare Janar na Kungiyar Kawancen Tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg, ya zargi Shugaban Rasha Vladmir Putin da tayar da zaune tsaye a Turai biyo bayan mamayar da kasarsa ta yi wa Ukraine.
Shi ma Firaministan Birtaniya Boris Johnson, ya bi sahun masu sukan Shugaba Vladimir Putin na Rasha a kan hare-haren da dakarun Rasha ke kai wa kan birnin Kharkiv na Ukraine.
- ’Yan mata, kada ku shiga harkar fim’
- ASUU: An tashi baran-baran a tattaunawar Ministan Ilimi da shugabannin dalibai
Yana magana ne a yayin wani taron maneman labarai na hadin guiwa tare da Firaministan Poland, Mateusz Morawiecki a babban birnin Poland din Warsaw.
Ya ce, a fili take karara, Vladimir Putin a shirye yake ya yi amfani da dabaru na dabbanci da kan-mai-uwa-da-wabi a kan fararen hula wadanda ba su ji ba kuma ba su gani ba a yakin da yake yi da Ukraine.
Firaministan na Birtaniya ya kuma ce duniya na ganin abin da ya kira bala’in da ke faruwaa nahiyar Turai.
Shi kuwa Firaministan na Poland cewa ya yi babban abin da za a mayar da hankali a kansa shi ne kara sanya wa Rasha takunkumi, sannan kuma ita NATO ta kara karfafa bangarenta na gabashi, wanda ke da iyaka da Ukraine da Rasha.
A nasa bangaren Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya zargi hukumomin Kyiv ne da laifin keta haddin dan-Adam a yankunan da kabilun Rasha suke a gabashin Ukraine, ba tare da gabatar da wata shaida ba.
Haka kuma ya ce abu ne da gwamnatin Rasha ba za ta taba lamunta ba a ce Amurka ta ajiye wasu makamanta na nukiliya a wasu kasashen Turai.