Kungiyar Tsaro ta NATO ta bukaci kasar China ta shiga cikin tattaunawar kayyade yawan makaman da kowace kasa za ta iya mallaka a wani kokari na dakile yunkurin kasar na fadada nukiliyarta.
Babban Sakataren Kungiyar NATO, Mista Jens Stoltenberg ya nuna damuwa kan yadda China take ci gaba da fadada makamashinta na nukiliya.
- Atletico Madrid ta lallasa Barcelona a gasar La Liga
- Bashin N100bn: APC ta zargi Finitiri da wawure kudin jama’a
A cewarsa, akwai bukatar kasar ta mutunta dokokin duniya wajen shiga tattaunawar kayyade yawan makaman don kauce wa hadarin da matakin nata kan iya haifarwa.
Stoltenberg a ganawarsa da Ministan Harkokin Wajen China, Mista Wang Yi, ta bidiyo, ya ce duk da kasancewar China ba ta cikin mambobin NATO amma yana da kyau ta mutunta dokokin duniya.
A zantawar tasu Stoltenberg ya ce akwai bukatar China ta rika bayyana wa duniya irin makaman da take mallaka ba tare da nuku-nuku ba.
Kuma ya kamata a ce ayyukanta na soji a fili take yin su sabanin yadda take boyewa.
China dai tana cikin kasashen da suke da karfin makamin nukiliya a duniya, sai dai NATO tana nuna fargaba a lokuta da dama game da rashin fayyace wa duniya matakin da ta kai a bangaren nukiliya.