✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nasarawa: Zanga-zanga ta barke bayan hukuncin kotun koli

Masu zanga-zanga sun rufe hanyar Lafia zuwa Jos.

Zanga-zanga ta barke a garin Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa, biyo bayan hukuncin da kotun koli ta yanke na tabbatar da zaben Gwamna Abdullahi Sule.

Magoya bayan jam’iyyar PDP sun rufe hanyar Lafia zuwa Jos, inda suka kone tayoyi don nuna fushinsu kan hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar Juma’a.

Zanga-zangar ta tilasta wa masu ababen hawa bin wasu hanyoyi a Lafia, don gujewa samun tsaiko ko shiga tashin-tashina.

Rundunar ’yan sandan jihar, ta aike jami’an tsaro wurin domin tabbatar da tsaro.

Tuni ’yan kasuwa da makarantu da ke yankin suka rufe sakamakon fargaba.

A ranar Juma’a ne kotun koli, ta yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar PDP, David Umbugadu, ya shigar na bukatar soke nasarar Gwamna Abdullahi Sule.