A wannan mako ne aka bayyana sakamakon zaben gwamnoni da wakilan majalisun jihohi da aka gudanar a jihohi 29 na kasar nan ranar Asabar da ta gabata.
Daga cikin wadanda suka samu nasara a cikin ’yan takarar Gwamna har da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i wanda ya samu kuri’u sama da miliyan daya wanda hakan ya ba shi damar ci gaba da mulkin Jihar Kaduna a karo na biyu.
Sai dai kuma wannan nasarar da Malam Nasiru ya samu ba ta zo da sauki ba, domin an yi ta tafka muhawara da cece-ku-ce game da takarar tasa, musamman da yake ya dauki mace Musulma a matsayin Mataimakiyarsa.
Wannan mataki da Gwamna Nasiru ya dauka ya haifar da zazzafar muhawara saboda tunda aka kirkiro Jihar Katsina daga Jihar Kaduna a 1987, ba a taba samun wani dan takarar Gwamna Musulmi da ya dauki Musulmi a matsayin Mataimakinsa a Jihar Kaduna ba sai a zamaninsa, saboda an mayar da tsayar da Musulmi da Kirista a matsayin ’yan takarar Gwamna da Mataimaki ya zama al’ada ko ma a ce ya zama kamar wajibi.
Wadansu mutane a ciki da wajen Jihar Kaduna suna ganin kamar Malam Nasiru ya kira wa kansa ruwa saboda wannan mataki da ya dauka, inda wadansu suka rika kartar kasa suna kurari suna cewa za su nuna masa kuskurensa. Sai dai kuma ga dukan alamu shi duk kurarin da aka yi ba su ba shi tsoro ba, saboda ya gamsu cewa ba don muzanta wa wadansu ya dauki wannan matakin ba, ya yi haka ne domin ya fifita cancanta fiye da duk wani abu a yayin da zai nada wani a kan mukami.
A yayin da ake zaton zaben na Jihar Kaduna zai zama tsakanin Musulmi da Kirista, sai aka wayi gari hakan bai kasance ba, domin an samu Musulmi da dama da suka zabi Jam’iyyar PDP, kuma akwai mabiya addinin Kirista da dama da suka zabi Jam’iyyar APC, hatta Babban Daraktan Kamfen na Gwamna El-Rufa’i Mista Ben Kure ma Kirista ne. Hakan ya nuna cewa masu zabe sun yi amfani da cancanta ne a yayin kada kuri’arsu ba wata manufa ta daban ba.
Yanzu dai an kammala zabe kuma Allah Ya ba Malam Nasiru El-Rufa’i nasara, wanda ya ba shi damar ci gaba da mulkin Jihar Kaduna a karo na biyu, abin da rage shi ne sai ya himmatu wajen ci gaba da ayyukan alherin da ya faro, kuma ya rungumi kowa ba tare da nuna bambancin jam’iyya ko kowane irin bambanci ba. Na ji dadi da shi kansa Malam Nasiru ya bayyana a jawabinsa na godiya cewa yanzu siyasa ta wuce kowa nasa ne a Jihar Kaduna kuma zai dauki kowa a matsayin daya.
Akwai bukatar Malam Nasiru ya duba kura-kuren da ya yi a yayin mulkinsa karo na farko domin ya gyara, zai yi kyau ya duba batun malamai da sauran ma’aikata da aka sallama daga aiki amma suka ce har yanzu ba a biya su hakkokinsu ba, duk da yake shi yana cewa an biya su. To tunda an samu tirka-tirka game da batun ya kamata ya bincika ya gano inda aka samu matsala domin a magance ta.
Haka kuma akwai bukatar ya sake duba batun wadanda aka rushe wa gidajensu a Kwalejin Alhudahuda da ke Zariya da nufin a taimaka musu da wani abu domin su samu wani matsugunin.
Akwai kuma bukatar ya rika sauraron shawarwari daga jama’a a kan wasu muhimmmam batutuwa da suka taso, kada ya yi saurin yanke hukunci sai ya tattauna sosai, domin gudun kada a maimaita abin da ya faru har aka rushe wa wadansu manyan mutane gidajensu saboda bambancin ra’ayin siyasa.
Ya kamata ya yi kokari ya ba marada kunya, domin wadansu suna ganin ya yi lambo ne ya sassauta wadansu matakai masu zafi da yake dauka domin yana so a sake zabensa a karo na biyu daga nan kuma sai ya juyo ya ci gaba da musguna wa wadansu tare da taka duk wanda ya daga masa yatsa. Sai dai kuma shi kansa ya fadi cewa shugabanci babban nauyi ne, to ya kamata ya kula sosai domin ganin ya sauke nauyin da aka dora masa.
Yanzu dai ci gaba kawai zai yi da shugabancin Jihar Kaduna domin ya riga ya gano bakin zaren, ya san inda duk wasu matsaloli suke. Sabanin a farkon mulkinsa inda har al’amarin ya ba shi mamaki ya ce, aikin Gwamna da wahala domin ba kamar aikin Minista da ya yi ba ne.
Zaben da al’ummar Jihar Kaduna suka sake yi masa har ma suka ba shi kuri’u fiye da wadanda suka ba Shugaba Buhari a zaben Shugaban Kasa da aka yi, ya nuna cewa mutanen jihar sun gamsu da salon mulkinsa kuma sun yarda zai iya dawo da martabar Jihar Kaduna a idon duniya, wanda zai zan sanya a karshen wa’adin mulkinsa insha Allahu kowa zai yarda cewa nasarar Nasiru ba asara ba ce saboda dimbin ayyukan alherin da ya gudanar. Muna fata Allah Ya taimake shi.
Su kuma al’ummar Jihar Kaduna su daure su ci gaba da bai wa Malam Nasiru hadin kai da goyon baya domin ya samu nasarar aiwatar da ayyukan da ya sanya a gaba domin raya Jihar Kaduna. Saboda ya dauko hanyar ciyar da Jihar Kaduna gaba yadda za ta zama abin sha’awa ga kowa.
Wadanda suke ganin ya munana musu su yi hakuri, domin shugabanci nagari ya gaji haka, dole ne a yayin da ake kokarin dadada wa wadansu sai an munana wa wadansu, abin da ba a so dai kawai shi ne shugaba ya yi wani abu da gangar domin ya musguna wa wadansu.