✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Napoli ta doke Juventus a wasan karshe na Copa Italia

Kungiyar kwallon kafa ta Napoli ta doke Juventus a wasan karshe na Copa Italia a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan sun tashi…

Kungiyar kwallon kafa ta Napoli ta doke Juventus a wasan karshe na Copa Italia a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan sun tashi canjaras babu ci.

Wannan nasarar ta bai wa Napoli damar lashe gasar a karo na shida a filin wasa na Stadio Olimpco da ke birnin Rome.

An tashi 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron gidan ne bayan ‘yan wasan Juventus din Paulo Dybala da Danilo sun barar da damarsu.

Wannan dai shi ne kambun farko da Napoli ta lashe tun shekarar 2014 kuma na farko wa kociyan kungiyar Gennaro Gattuso wanda ya maye gurbin Carlo Ancelotti watan Disamban 2019.