✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nan da ’yan makonni za a magance matsalar tsaro a yankinmu —Wase

Wase ya bai wa jama'ar mazabarsa tabbacin cewa nan da makonni kadan za a kawo karshen kalubalen tsaro

Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Ahmed Idris Wase, ya tabbatar wa al’ummar mazabarsa da ke fuskantar hare-haren ’yan bindiga cewa nan da makonni kadan za a kawo karshen kalubalen tsaro.

Ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da ya ziyarci Sarkin Wase, Muhammad Sambo Haruna a fadarsa, domin jajanta masa da kan harin baya-bayan nan a yankin.

A sanarwar da babban sakataren yada labaransa, Umar Muhammad Puma, ya fitar a ranar Litinin, Wase ya ce nan ba da dadewa ba za a kawo karshen hare-haren da ’yan bindiga ke kai wa wasu al’ummomi a yankin.

Ya shaida wa basaraken da al’ummar mazabar cewa Gwamnatin Tarayya na daukar tsauraran matakai daban-daban domin inganta tare da dakile maimatuwar hakan da ma saura matsalolin tsaro.

Ya ce: “Ina so in tabbatar muku da mai martaba cewa ana daukar tsauraran matakan tsaro don tabbatar da tsaron mutanenmu da dukiyoyinsu.

“Ba a tattauna batutuwan tsaro da dabarunsu a bainar jama’a, amma ina tabbatar muku nan da makonni kadan za a kawo karshen kalubalen tsaro.

“Ina kira ga daukacin al’ummar Wase da mu yi aiki tare, mu hada kawunanmu domin ganin an yi abin da ya dace, tsaro da tsaron al’ummarmu shi ne babban abin da muka sa gaba, kuma duk abin da bai kai haka ba abu ne da ba za a amince da shi ba.

“Ina so in karfafa wa jama’ata gwiwa da su kasance masu addu’a da yin tsayin daka da kuma tabbatar da cewa mun bai wa jami’an tsaro duk goyon bayan da za su bukata domin cafke wadanda ke kai wadannan hare-hare”.

Idan dai za a iya tunawa a ’yan kwanakin nan ne aka samu rashin zaman lafiya a wasu sassa na mazabar Wase, inda aka yi asarar rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa.

Da yake mayar da martani, Sarkin ya yaba da kokarin Mataimakin Shugaban Majalisar na magance ayyukan ’yan bindiga da sauran miyagun laifuka a mazabar.

Ya kuma tabbatar masa da goyon bayansa sannan ya bukace shi da ya ci gaba da tallafa wa marasa galihu da marasa aikin yi a cikin al’umma.