Ministan Lafiya, Dakta Osagie Ehanire akwai alamun yunkurin da Najeriya take yi na samo allurar rigakafin COVID-19 zai haifar da da mai ido nan da watan Janairun 2021.
Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba lokacin da yake yi wa ‘yan jarida jawabi, jim kadan da kammala taron Majalisar Zartarwa ta kasa karo na 28 ta fasahar bidiyo a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja.
- Tsohuwa mai shekara 90 ta fara amfani da rigakafin COVID-19 na Pfizer
- Rigakafin COVID-19 na daf da shiga kasuwa
A cewar Ministan, tuni tattauna ta yi nisa tsakanin su da kamfanoni da kuma kasashen da suke zama jagaba a harkar samar da rigakafin.
Sai dai ya ce suna duba kalubalen kudaden adana alluran musamman irin wadannan tun ma kafin su kai ga sayo su.
Osagie ya ce, “Tuni muka kafa kwamitin kwararru dake aiki ba dare ba rana a kan rigakafin.
“Mun cimma matsaya da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da takwarar ta ta Hadakar Kasashe Domin Samar da Rigakafi (GAVI) kan samun alluran da zarar sun shiga kasuwa.
“Kun san sabbi ne, kuma masu samar da su ba za su yi wasa ba.
“Tabbas manyan kasashe wadanda sune ke sarrafa wadannan magungunan dole su ba kan su fifiko, amma muna sa ran matsin lambar da WHO da GAVI za su yi musu zai sa su waiwaye mu,” inji ministan.
A watan Nuwamba ne dai kamfanonin Pfizer-BioNTech suka samar da rigakafin da suka ce tana da tasirin kusan kaso 90 cikin 100 wajen magance cutar, kuma tuni wasu kasashen suka fara amfani da ita a matsayin gwaji.