Jam’iyyar APC mai mulki ta ba ’yan Najeriya tabbacin cewa nan ba da jimawa ba kasar za ta fita daga masassarar tattalin arzikin da ta fada.
Jam’iyyar ta kuma ce Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da yin iya bakin kokarin ta wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa.
Sakataren kwamitin riko na jami’iyyar, Sanata John Akpanudoedehe ne ya bayar da tabbacin a ranar Alhamis cikin sakon sa na Kirsimeti, yana mai cewa annobar COVID-19 ce ta yi sanadiyyar fadawar kasar cikin halin da take ciki a yanzu haka.
Sanata John ya ce, “Kamar kowacce kasa, annobar COVID-19 ta jefa Najeriya cikin halin matsin tattalin arziki, amma nan ba da jimawa ba, la’akari da matakan da Gwamnatin Tarayya ke dauka za mu fita daga ciki.
“Yana da kyau mu lura matuka cewa tabarbarewar da muka shiga ta biyo bayan shafe tsawon rubu’in shekara har guda 12 tattalin arzikin yana samun tagomashi.
“Tun daga iftila’in sace dalibai da aka samu a makarantun sakandiren Chibok, Dapchi da Kankara, gwamnatin Buhari ba ta taba yin kasa a gwiwa ba wajen lalubo bakin zaren, ko da makamanciyar wannan matsalar ta taso,” inji sakataren na APC.
A kwanakin baya ne dai Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta tabbatar da cewa Najeriya ta sake fadawa masassarar tattalin arziki a karo na biyu cikin shekaru hudu kenan, duka karkashin mulkin APC da Buhari ke yi wa jagoranci.