✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Namiji ya kwace kambun mafi dadewa a girki na duniya daga hannun ’yar Najeriya

Wani dan kasar Ireland ne ya kwace kambun bayan ta yi wata 5 tana rike da shi

Kundin banjinta na duniya na Guinness World Records ya tabbatar da cewa wani mai girki dan asalin kasar Ireland, Alan Fisher, ya karbe kambun mafi dadewa yana girki a tarihin duniya.

Hakan dai ma nufin mutumin ya kwace kambun daga hannun ’yar Najeriya, Hilda Baci, wacce kundin ya tabbatar mata da kambun a watan Yunin da ya gabata.

Kambun na Guinness ne ya sanar da hakan a dandalinsa na X a ranar Talata.

Guinness ya ce, “An karbe kambun dadewa ana girki na duniya daga hannun ’yar Najeriya, sarauniya Hilda Baci.

“Alan Fisher daga kasar Ireland ya yi  girki na tsawon sa’o’i 119 da minti 57 a wani gidan abinci da ke kasar Japan,” in ji shafin.

Hakan dai na nufin ya zarce tarihin da Hilda ta kafa da sama da awa 24.

Bugu da kari, Alan ya kuma karbi kambun mafi dadewa yana gasa burodi a duniya inda ya yi awoyi 47 da minti 21, inda ya zarce mai rike da kambun a yanzu, Wendy Sandner, Ba’amurike mai awa 31 da minti 16.

Alan, a cewar Guinness ya lashe kambunan guda biyu ne a lokaci daya, inda ya shafe, jimillar sa’o’i 160 a dakin girki kafin ya kafa tarihin.

A baya dai Hilda ta yi yunkurin kafa tarihin yin girkin awa 100 ne, amma baya tantancewa, kundin ya cire awa bakwai daga ciki.

Mai kimanin shekara 26 a duniya, Hilda ta shiga dakin girki ne tun a ranar Alhamis, 11 ga watan Mayu, sannan ta ci gaba da girki har zuwa ranar Litinin, 15 ga watan.

A lokacin dai, ta girka abinci sama da kala 100, sannan ta ce ta kashe sama da miliyan 100 a gasar.