✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Miji ya kashe matarsa saboda taliyar yara

Mijin ya dawo daga aiki ne ya tarar matar ta dafa taliyar yara.

Wani magidanci ya hallaka matarsa saboda taliyar yara a yankin Olota da ke Karamar Hukumar Alimosho a Jihar Legas.

Ana zargin magidancin ya yi wannan aika-aika ne bayan da ya dawo daga aiki ya samu matarsa ta dafa taliyar yara maimakon abincin da ya fi so.

Wata majiya da ta bukaci a saka sunanta saboda tsaro, ta ce mijin ya bar matar kwance bayan ya doke da dutse a kanta.

Majiyar ta ce wani makwabcin magidancin ne ya kira magidancin ya sanar da shi matarsa na cikin wani yanayi.

Makabtan ne suka garzaya da matar zuwa asibiti inda a can ne aka tabbatar da rasuwarta.

Shaidu sun ce ’yan sanda sun cafke miji inda suna gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru a tsakaninsa da matarsa.

Amma rundunar ’yan sandan jihar Legas ta ce kawo yanzu ba a tabbatar da cewar mijin ne ya kashe matar ba.

Kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin ya ce suna kan bincike kuma da zarar sun kammala za su bayyana wa jama’a sakamakon binciken da suka samu.