✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Namiji na takarar Shugabar Mata ta Kasa a APC

Ya ce tun yana yaro ya dauki al'amuran da suka shafi mata da muhimmanci.

Wani matashi mai suna Ameer Sarkee mai shekara 26, ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar Shugabar Mata a Jam’iyyar APC.

Matashin ya ce ya fito takarar ce domin namiji ne ya kamata ya rika lura da al’amuran mata a kowane lokaci.

Ameer, wanda ya taba tsayawa takarar Shugabar Mata a Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kano a 2019 ya sha kaye, ya ce a wannan karo ba zai bari a kayar da shi ba saboda tun yana yaro batutuwan da suka shafi mata ya fi son aiwatarwa.

“Tun ina karamin yaro idan na ga mace tana bukatar taimako nakan yi koƙarin taimaka mata – kamar daukar kaya ko sayo wani abu – kuma hakan ne ya sa nake son zama Shugaban Mata na jam’iyyarmu,” inji shi.

“Wadansu mutane suna tambaya ta abin da ya sa nake takarar kujerar Shugabar Mata, amsar da nake ba su ita ce ‘Allah Ya halicci namiji domin ya zama mai lura da lamuran mata,” inji Ameer.

Matashin dan asalin Jihar Kano da ke sayar da tufafi ya ce abin da yake kona masa rai shi ne yadda mata kan yi fitar-dango domin kada kuri’a a lokutan zabe amma da zarar sun gama sai masu mulki su kawar da kai daga sha’anin cigabansu.

Ya ce idan ya yi nasara zai tabbatar da ganin an kara jin muryoyin mata a sha’anin siyasa da mulki.

Dangane da kalubalen da yake fuskanta a takarar, Ameer ya ce yana fatan matan Jam’iyyar APC za su amince su zabe shi duk da yake shi namiji ne.

Matashin dan siyasar ya ce: “A lokaci guda kuma ina samun kwarin gwiwa daga wurin mata, ko da a jiya sai da wasu kungiyoyin mata suka zo don jaddada goyon baya gare ni sannan da dama daga cikinsu suna goyon bayana a shafukan sada zumunta.”

Duk da yunkurin da Ameer ke yi don ganin ya inganta lamuran mata, a yanzu ba shi da aure amma ya ce yana shirin angwancewa.