Wata nakiya da mayakan Boko Haram suka binne a kan titin Pulka/Firgi da ke Karamar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno, ta hallaka manoma bakwai a cikin wata motar haya.
A safiyar ranar Litinin, 29 ga watan Janairu, 2024, abin motar da ke dauke da wadanda abin ya shafa ta bi ta kan nakiyar da ’yan ta’addan suka dasa.
Majiyoyin sun ce an tabbatar da mutuwar fasinjoji bakwai wadanda manoma ne da direban motar a yayin da wasu bakwai suka samu munanan raunuka.
’Yan ta’addan sun dauki wannan salon ne ganin cewar dakarun sojin Najeriya sun dukafa ka’in da na’in don ganin bayansu ko ta halin kaka.
- Mijin Layla Ali Othman zai maka Sadiya Marshall a Kotu
- Jiragen soji sun kashe ’yan bindiga 30 a Birnin Gwari
Majiyoyin tsaro na nuna cewar, nakiyoyin da aka dasa a baya-bayan nan sun yi sanadin salwantar rayukan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba — galibinsu yara mata a jihar Borno.
“Wadannan bama-bamai, da akasarinsu na cikin gida ne, su ne ’yan ta’addan suka rika amfani da su tun lokacin da suka fara tada kayar baya a yankin nan na Arewa maso Gabas da suka kai ga halaka dubban jama’ar da ba su ji ba, ba su gani ba,” in ji majiyar.