✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mijin Layla Ali Othman zai maka Sadiya Marshall a Kotu

Mijin Layla Ali Othman ya ce idan har Sadiya Marshall ba ta kawo hujjojin da take zargin matarsa ba, to ta tabbata sai ta je…

Mijin Layla Ali Othman, Yusuf Adamu Gagdi, ya yi barazanar maka kawarta Sadiya Marshall a kotu saboda bata wa matarsa suna.

Yusuf Gagdi wanda dan Majalisar Wakilai ne, ya yi wannan barazana ne bayan wani bidiyon da Sadiya Marshall ta saki, wanda a ciki ta yi wa Layla wankin babban bargo, har da zargin cin amanar aure.

Sadiya “Da bakin da ta yi wa matata wadannan kage za ta dawo ta karyata kanta. Na san idan ta yi kwana biyu a tsare dole za ta fito da hujjojin da take ikirarin tana da su,” in ji Honorabul Yusuf Gadgi, a shafinsa na X.

A bidiyon da Sadiya ta ce martani ne sabdoa abubuwan da Layla ta yi mata sun kai ta bango, ta zargi Laylan da alaka da tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho na kasa, Abdulrasheed Maina, wanda ke tsare a gidan yarin Kuje da ke Abuja.

Sadiya Marshall ta kuma zargi Layla Ali Othman da yin gulman ta da Maina, inda ta yi barazanar idan Layla ba ta fita daga sabgarta ba, to za ta saki hotunan da kawar tata ta tuttura, da ma muryoyin hirarsu da Maina.

A mijin Layla Ali Othman, ya ce, “Idan har (Sadiya Marshall) ta kasa kawo hotuna da bidiyo da rabutattun sakonnin matata da take ikirari ba, to zan tabbatar ta je gidan yari… iyalina ba abin wasa ba ne.”

Dan majalisar ya bayyana hakan ne a amsarsa ga wani mai suna Unknown a X, wanda ya tambaye shi cewa, “Ka ji abin da Sadiya ta ce kuwa? Shin wace kyautar zagayowar ranar haihuwa za ka yi wa mai dakinka?”

Bayan amsar da dan majalisar ya bayar ne Unknown ya kara da cewa, “Alhamdullah, abin da nake son ji ke nan, saboda hakan ya zama darasi ga wasu… Fatan alheri.”