✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nakasa ba kasawa ba ce: Mu tashi mu nemi halaliya!

A makon da ya gabata, makaranta shafin nan da dama sun bugo waya, wasu kuma sun turo da sakonnin tes, suna nuna gamsuwa da wannan…

A makon da ya gabata, makaranta shafin nan da dama sun bugo waya, wasu kuma sun turo da sakonnin tes, suna nuna gamsuwa da wannan tsokaci. daya daga cikin wadannan dinbim masu karatu, shi ne MALAM IBRAHIM ABUBAKAR, wanda ya nuna cewa tsokacina bai Ambato nakasassu ba, wadanda su ma suna cikin mabukata tallafi da taimako. Wannan dalili ya sanya a yau, ni GIZAGO (08065576011) zan maida hankali kan nakasassu, sannan in bijiro da hanyoyin da ya kamata a taimaka masu, kamar kuma yadda zan bayyana wuraren da su da kansu za su taimaki kansu, domin kuwa masu salon magana suna cewa, nakasa ba kasawa ba ce:

g Naqasa ba kasawa ba ce, kamar yadda wannan bawan Allah ya tabbatar!“Assalamu alaikum, Gizago; da fatan an sha ruwa lafiya, amin. Gizago, na dade ina bin shafinka kuma ina jin dadin shi. Na ga rubutunka na wannan satin a kan mabukata, sai dai ban ga nakasassu a cikin rubutunka ba amma duk da haka mu ma a madadin guragu da sauran nakasassu; ina nema masu alfarmar su ma a taimaka masu, musamman da jarin ko tireda ne, domin mu samu mu rika dogaro da kanmu a hankali, maimakon ba mu sadaka. Don Allah a duba mana wannan sako, alfarmar Mai Makkah da Madina, gatan kowane mai Sallah. Ka huta lafiya, inda ka ga gyara, ka taimaka ka gyara mani. Na gode.” – Daga Ibrahim Abubkar (08093275753).
Madalla da wannan sako naka, Malam Ibrahim. Kuma tabbas yana kan hanya kuma nakasassu na matukar bukatar tallafi kamar yadda su ma mabukata masu lafiya suke da ita. Al’amarin kasar tamu ce mai wahalar sha’ani, domin kuwa akasari kusan komai a baibai muke gudanar da shi. Ga shi dai al’ummar Najeriya na da kokarin aiwatar da addini, amma kash, mun yi tasgaro wajen tallafar al’umma.
A Najeriya ne za ka ga Musulmi da kokarin ibada da kokarin gina masallaci da yi masa kwaskwarima, amma sai kalilan ne ke maida hankali wajen ciyarwa da tufatarwa da ma tallafar mabukata da nakasassu. Haka labarin yake ga mabiya addinin Kirista. Za ka ga mabiyi yana kokarin zuwa coci da kokarin gina ko inganta coci, amma tallafin mabukaci ko nakasasshe, abin sai a hankali.
A gaskiya lokaci ya yi da ya kamata mu sake tsari, ya kamata mu kawo sauyi a rayuwarmu. Kamata ya yi a kowace unguwa, a dauki rijistar nakasassu, a tsara yadda za a rika taimaka masu, yadda ba lallai ne sai sun yi bara ba, domin kuwa duk wanda Allah Ya halitta, komai nakasarsa, yana da wata baiwa ta musamman da zai iya amfani da ita domin ya samu abin saka wa bakin salati.
Misali, ya dace masallatanmu da coci-coci su kasance suna da gidauniya, ta yadda duk wani nakasasshe da ke unguwa za a san da zamansa, sannan a kula da yadda rayuwarsa ke gudana. Misali, kamar guragu, za a iya daukar nauyin koya masu sana’o’in hannu, kamar gyaran mota, gyaran babur ko aikin kafinta ko kuma saka da sauran sana’o’i, kamar tireda da sauransu. Haka su ma makafi da kurame, za a iya daukar nauyin karatunsu, idan suna da kuruciya, yadda za su yi karatu mai zurfi, su kasance masu taimakon al’umma a fagage daban-daban na rayuwa.
Gwamnatocin kananan hukumomi da na jihohi da uwa-uba ta tarayya, ya kamata a cikin kowane kasafin kudi na kowace shekara, su ware shiri na musamman na tallafar nakasassu. A nan, ba ina nufin a rika ba su kudi ko tiyoyin hatsi da kudin cefane ba. A’a, a sama masu wani tsari na musamman, kamar dai yadda aka shawarta a baya, ta yadda za su kasance masu amfani da baiwar da Allah Ya ba su, wajen sama wa kansu abin rayuwa; ta yadda su ma sai dai su ba wani, ba wai lallai su dogara da wani ya ba su ba.
Sai dai kuma bayan an bugi jaki, ya kamata kuma a bugi taiki, bayan an bi ta barawo kuma ya kamata a bi ta mabi sawu. Ma’ana, bayan mun tuntubi al’umma da gwamnati, ya kamata mu waiwayi su kansu nakasassun, domin a jawo hankalinsu, yadda za su amince da cewa nakasar nan da ke jikinsu ba kasawa ba ce.
Ya kai mai dauke da wata nakasa ko kuma wanda ya rasa wani bangare na jikinsa, kada ka sake zuciyarka ta mutu. Wannan nakasa da ke jikinka, ba kasawa ba ce, hasali ma kalubale ne a rayuwarka. Idan ka yarda da maganata, bari in sanar da kai cewa zuciyarka rayayya ce, tangaran take, kwakwalwarka ingantatta ce, cike take da baiwar da Allah Ya kimsa a cikinta, madamar ka yi amfani da ita yadda ya dace, babu shakka ba za ka kasance mabaraci ba, koda kuwa a nannade kake, ba ka iya mikewa da kafafunka.
Inda gizo ke sakar shi ne, mu a nan, musamman kasar Hausa, da zarar an jarabci mutum da gurguntaka, ko da makanta, shi ke nan sai zuciya ta langabe, mu ce sai dai mutum ya yi bara, alhali idan mun duba, akwai wata baiwa da Allah Ya yi masa, wacce da ita zai iya dogaro da kansa, ya samu abin rayuwa. Wani za ka ga kila kafarsa daya ce kawai ta dan tasgade, sauran jikinsa daidai suke, amma shi ke nan ya samu lasisin bara. Wani kuwa watakila hannu daya ne kadai ya murgude, shi ke nan sai bara. Lallai ya zama dole mu canza salo, sauran al’ummomin duniya tuni suka ci gaba, ba su daukar makaho ko gurgu a matasyin mai kasawa.
Ba sai mun je da nisa za mu ga misali ba, ni kaina a unguwarmu, akwai wani gurgu mai suna Mamman, kusan yaya ne a gare ni, a haka aka haife shi, kafafuwansa a murde, bai taba takawa da su ba, amma ya yi makarantar firamare, daga nan ya shiga garejen gyaran mota. Ya koyi gyaran mota, ya kware sosai, inda ya bude shagonsa na kansa a garin kankara, Jihar Katsina. Har Allah Ya amshi ransa bai bara. Maimakon bara ma, wasu da dama sun dogara da shi, yana da iyali, yana da yara da suka koyi sana’ar daga wajensa.
A Katsina, a tashar motar KTSTA, akwai wani makaho da ake wa lakabi da Malam Mara Ido. Bai bari rashin ido ya kashe masa zuciya ba, ya yi ilimin zamani, ya yi na addini kuma ya yi zama a garuruwa daban-daban, yana jin yaruka da dama. Sana’rsa sayar da maganin gargajiya kuma da ita yake biya wa kansa da iyalinsa bukata, har ma yana taimakon wasu.
A garin Maraba, Jihar Nasarawa, akwai wani gurgu dan asalin Jihar Kano, rarrafe yake saboda rashin kafafu, amma duk da haka, maimakon ya yi bara, sai ya koyi sana’ar gyaran takalma. A kansa yake dora kwandon aikinsa, ya yi rarrafe cikin mutane yana gyara masu takalma, yana samun abin rufin asiri.
A fagen ilimi, makafi na yi zarra, kurame na yin zarra, inda wasu ke zama malaman makaranta, wasu kuma suna aikin jarida da sauran ayyukan fasaha. Don haka nakasa ba kasawa ba ce, ya kamata mu sanya haka a tunanin nakasassunmu, mu taimaka masu da hanyoyin da suka dace, ta yadda za su rika cin gajiyar boyayyun baiwowin da Allah Ya yi masu. Allah sa mu dace, amin!

“Assalamu alaikum, Gizago; da fatan an sha ruwa lafiya, amin. Gizago, na dade ina bin shafinka kuma ina jin dadin shi. Na ga rubutunka na wannan satin a kan mabukata, sai dai ban ga nakasassu a cikin rubutunka ba amma duk da haka mu ma a madadin guragu da sauran nakasassu; ina nema masu alfarmar su ma a taimaka masu, musamman da jarin ko tireda ne, domin mu samu mu rika dogaro da kanmu a hankali, maimakon ba mu sadaka. Don Allah a duba mana wannan sako, alfarmar Mai Makkah da Madina, gatan kowane mai Sallah. Ka huta lafiya, inda ka ga gyara, ka taimaka ka gyara mani. Na gode.” – Daga Ibrahim Abubkar (08093275753).