More Podcasts
Domin sauke shirin latsa nan
A duk lokacin da hukumar zabe ta ayyana wani zabe a matsayin wanda bai kammalu ba akan samu ce-ce-ku-ce, ganin cewa a cikin ’yan takarar da suka tsaya zaben akwai wanda ya fi samun yawan kuri’u.
A shekarun bayan nan an samu zabuka da dama aka ayyana a matsayin wadanda ba su kammalu ba wato ‘inconclusive’ a turancin Ingilishi; Na karshe shi ne zaben gwamnan Jihar Anambra mai cike da turka-turka.
Shin me ke sa zabe ya zama ‘inconclusive’, yaya ’yan Najeriya ke kallon zaben da aka ce ya zama ‘inconclusive’, sannan me dokar kasa ta ce a kansa?
Shirin Najeriya A Yau na dauke da wadannan bayanan har da kari. A yi sauraro lafiya.