✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Najeriya za ta yi dokar hukunta masu tsangwamar mata masu Hijabi

'Nan da karshen 2021 za a sanya wa dokar hannu'

Najeriya za ta yi dokar hukunta masu nuna wariya ko wulakanta mata masu sanya Hijabi.

Gamayyar Kungiyoyin Musulunci a Najeriya ta bayyana haka a jawabinta na Ranar Hijabi ta Duniya ta 2021, inda ta ce aibata mata masu lullubi ko tsangwamar su tauye musu ’yancin da dokar kasa ta ba su ne.

Don haka ta bukaci bangaren Majalisa da ta kafa dokoki hana wariya ko aibanta mata Musulmi masu sanya Hijabi a wuraren aiki.

“Muna fatar ganin Majalisar ta amince da wannan da wuri; sannan dokar ta ayyana hukunci ga duk mai wulakanta ko ya aibata ko tauye hakkin ko ’yancin duk wata mace mai lullubi kamar kowane dan kasa,” inji ta.

Babbar jami’ar Kungiyar, Rukayyah Sindi, ta kuma bukaci a yi gyara ga “tsarin tufafin wuraren aiki da makarantu ta yadda mata Musulmai za su iya sanya hijabin da ya dace ba tare da an nuna musu wariya ba.”

Da take kokawa kan yadda wasu makarantu musamman a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya ke hukunta dalibai saboda sun sanya hijabi a kan kayan makaranta, Rukayyah ta ce dokar Najeriya ta ba wa kowa ’yancin yin addininsa, kuma addini ne sanya hijabi ga mace Musulma.

Don haka ta yi roko ga bangaren Shari’a da ya rika gaggauta yanke hukunci a kan duk masu tauye ’yancin mata saboda sun sanya hijabi.

Jawabin na Ranar mai taken kawo karshen kyamar Hijabi a Duniya (#Endhijabophopia globally), ya yi kira ga al’umma da su fahimci cewa sanya hijabi addini ne ba kayan ado ba.

Kakakin kungiyar, Rahmatu Sani, ta ce sabuwar dokar sanya hijabin za ta sa hukumomin tsaro da kamfanoni masu zaman kansu sauya tunani game da hana ma’aikatansu mata sanya hijabi a lokacin da suke bakin aiki.

Ta bayyana cewa kungiyar na da kwarin gwiwa cewa Majalisar Tarayya za ta amince da dokar kafin karshen shekarar 2021.

“Mun sha zuwa da wannan bukata Majalisa domin samun goyon bayanta, kuma mun samu tabbacin cewa kafin karshen wannan shekara za a yi wani abu kwakkwara.

“Duk da cewa an yarda mu yi addininmu, amma kuma muna bukatar mu yi lullubi yadda ya kamata cikin ’yanci,” kamar yadda ta bayyana.