✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya za ta sayar wa da kasashe hudu wutar lantarki

Wasu kasashe hudu a nahiyyar Afirka sun fara duba yiwuwar hada hannu domin sayen wutar lantarki daga Najeriya. Kasashen da ke neman sayen wutar lantarkin…

Wasu kasashe hudu a nahiyyar Afirka sun fara duba yiwuwar hada hannu domin sayen wutar lantarki daga Najeriya.

Kasashen da ke neman sayen wutar lantarkin a kasar da ake yi wa kallo a matsayin uwa maba da mama a nahiyyar Afirka, sun hada da Nijar, Togo, Benin da Burkina Faso.

Shugaban Kamfanin Tunkudo Lantarki na Najeriya (TCN) Sule Abdulaziz wanda ke zaman Shugaban Hukumar Gudanarwa ta Hadakar Kamfanonin Lantarki da ke Yammacin Afirka (WAPP), shi ne ya bayyana hakan yayin wani taro da aka gudanar a wannan mako.

Yana mai cewa ana sa ran kasashen hudu za su sayi lantarkin ne kan wani sabon tsari na ‘North Core’ da aka ware wa dala miliyan 570 da ake kan ginawa yanzu.

Aikin na ‘North Core’ Bankin Duniya, Hukumar Raya Kasashe ta Faransa da kuma Bankin Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ne suka bayar da tallafin ginawa, kuma ana sa ran kammala shi a cikin shekaru biyu masu zuwa.

Kamar yadda sashen Hausa na Gidan Rediyon Faransa RFI ya ruwiato, Abdulaziz ya ce kasashen sun yanke shawarar sayen wutar lantarki ce wacce ba a amfani da ita a Najeriya.

Kasar Najeriya wacce ta kasance tana fama da karancin wutar lantarki a kowane fanni, ta jima tana sayar da wutar lantarki ga kasashen Jamhuriyyar Benin, Togo da Nijar tsawon shekaru.

Sai dai Abdulaziz ya ce kasar za ta ci gajiyar wannan kasuwancin domin samun kudaden shiga da kuma samar da ayyukan yi..