Wasu kasashe hudu a nahiyyar Afirka sun fara duba yiwuwar hada hannu domin sayen wutar lantarki daga Najeriya.
Kasashen da ke neman sayen wutar lantarkin a kasar da ake yi wa kallo a matsayin uwa maba da mama a nahiyyar Afirka, sun hada da Nijar, Togo, Benin da Burkina Faso.
- Mazauna Saudiyya 60,000 ne kadai za su yi aikin Hajjin bana
- Mun cire ’yan Najeriya 10.5m daga kangin talauci —Buhari
Shugaban Kamfanin Tunkudo Lantarki na Najeriya (TCN) Sule Abdulaziz wanda ke zaman Shugaban Hukumar Gudanarwa ta Hadakar Kamfanonin Lantarki da ke Yammacin Afirka (WAPP), shi ne ya bayyana hakan yayin wani taro da aka gudanar a wannan mako.
Yana mai cewa ana sa ran kasashen hudu za su sayi lantarkin ne kan wani sabon tsari na ‘North Core’ da aka ware wa dala miliyan 570 da ake kan ginawa yanzu.
Aikin na ‘North Core’ Bankin Duniya, Hukumar Raya Kasashe ta Faransa da kuma Bankin Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ne suka bayar da tallafin ginawa, kuma ana sa ran kammala shi a cikin shekaru biyu masu zuwa.
Kamar yadda sashen Hausa na Gidan Rediyon Faransa RFI ya ruwiato, Abdulaziz ya ce kasashen sun yanke shawarar sayen wutar lantarki ce wacce ba a amfani da ita a Najeriya.
Kasar Najeriya wacce ta kasance tana fama da karancin wutar lantarki a kowane fanni, ta jima tana sayar da wutar lantarki ga kasashen Jamhuriyyar Benin, Togo da Nijar tsawon shekaru.
Sai dai Abdulaziz ya ce kasar za ta ci gajiyar wannan kasuwancin domin samun kudaden shiga da kuma samar da ayyukan yi..