✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Najeriya za ta yi nasarar gwajin rigakafin COVID-19 —Bill Gates

Shahararren attajirin duniya da ke kan gaba wajen yaki da annobar COVID-19, Bill Gates, ya ce za a yi nasarar amfani da rigakafin annobar wajen…

Shahararren attajirin duniya da ke kan gaba wajen yaki da annobar COVID-19, Bill Gates, ya ce za a yi nasarar amfani da rigakafin annobar wajen yakar ta a Najeriya.

A zantawarsa da kafar yada labarai ta Cable, attajirin ya yi tsokaci kan yadda a baya aka sanya tsoro a zukatan jama’a a kan allurar rigakafin cutar shan inna a Najeriya.

Ya ce da hadin gwiwar kafafen yada labarai da shugabannin siyasa da na addinai za a kawar da tsoro da shakka da ke zukatan jama’a game da maganin rigakafin COVID-19.

“Haka aka yi ta yada jita-jita a kan maganin rigakafin kyanda wanda abun takaicin shi ne tsoro ya hana iyaye da dama kai ‘ya’yansu a yi musu allurar rigakafin.

“Irin wannan jita-jitar aka yi ta yadawa a kan rigakafin cutar shan inna a shekarar 2003, sai dai a lokacin da yawa daga cikin shugabannin addinai da sarakuna irinsu Sarkin Musulmi a Sakkwato da Sarkin Kano sun yi rawar gani wajen wayar da kan al’umma bayan da suka fahimci maganin rigakafin ba shi da illa.

“Sun yi tsayin daka kwarai ta yadda suka hana cutar shan innar kama yara tana shanye musu hannaye da kafafu tana mayar da su guragu.

“Don haka idan maganin rigakafin COVID-19 ya iso ku  sani cewa tabbas yana da shaidar sahihanci daga kasashen duniya.

“Za kuma mu bukaci amincewar shugabannin addinai da kafafen yada labarai da ‘yan siyasa da sashen wasanni da na  kasuwanci ta yadda jama’a da dama za su karbi maganin rigakafin kuma cutar ta kau.

“Na yaba da abin da Alhaji Aliko Dangote ya yi na yakar annobar ta hanyar karfafa rundunar yaki da ita.

Kazalika a sassan gabashin  Afirka an yi kokari kwarai ta yadda aka samar da ingantaccen maganin annobar na ‘Dexamethasone’. Wannan abun a yaba ne”, inji shi.

Bill Gates ya kara da cewa idan maganin rigakafin ya iso za a tattauna da shugabannin kasashen Afirka domin tunkarar lamarin.

A cewarsa, darussan da aka koya a lokacin rigakafin cutar shan inna za su ba da damar samun nasarar rigakafin COVID-19 a Najeriya.