✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya za ta iya daukar nauyin gasar Kofin Duniya ta 2030 – Segun Odegbami

Tsohon dan wasan Najeriya, Cif Segun Odegbami ya ce Najeriya za ta iya daukar nauyin gasar cin Kofin Duniya ta shekarar 2030. Segun wanda shi…

Tsohon dan wasan Najeriya, Cif Segun Odegbami ya ce Najeriya za ta iya daukar nauyin gasar cin Kofin Duniya ta shekarar 2030.

Segun wanda shi ne dan takarar Gwamnan Jihar Ogun a karkashin Jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP) ya ce shirye-shirye kawai ya kamata a fara da wuri.

Odegbami ya yi wannan jawabi ne lokacin da yake gabatar da makala a wajen taron tunawa da Deji Tinubu a Jihar Legas mai taken: “Habaka Bangarorin da za su Bunkasa Harkokin Wasanni, da Sanya Hannun Masu Dukiya.”

Ya ce “Maganar gaskiya ita ce idan har an samu sa masu hannu da shuni sun tallafa da kuma tsare-tsare, za sa samu nasara sosai a harkokin wasanni. A Jihar Legas an fara samun ci gaba ne a bangaren wasanni a zamanin gwamnatin Fashola domin mutum ne mai son wasanni, kuma irinsu ake bukata.”

“Ina da niyyar gina wani katafaren filin wasa a Jihar Ogun wanda zai amfani masu tasowa. Sannan burina shi ne Najeriya ta dauki nauyin gasar cin Kofin Duniya ta shekarar 2030,” inji shi.

Odegbami ya ce da ilimi da wasanni kamar Danjuma ne da Danjummai, domin daya ba zai yiwu ba sai da dayan.

Ya ce rashin sanin riba da dimbin damar da suke cikin wasanni ne ya sa mutane da yawa suke sakin layin wasanni, sai ya yi kira ga matasa su rumgumi harkokin wasanni.