Hukumar Agajin Gaggawa ta Najeriya NEMA, ta tabbatar da cewa za a fuskanci matsalar ambaliyar ruwa a daminar bana.
Shugaban hukumar, Mustapha Ahmed ne ya bayyana haka ranar Litinin a Abuja, lokacin wani taro da hukumar ta shirya.
Duk da hukumar ba ta fayyace wuraren da ambaliyar za ta fi shafa ba, amma ta ce shiryawa da wuri zai taimaka wurin rage barnar da ambaliyar za ta iya haifarwa.
A daminar da ta gabata an samu mummunar ambaliya a sassan Najeriya daban-daban, lamarin da ya yi sanadin rayuka da dukiya mai dimbin yawa.
A kan haka ne hukumar ta shirya taron kara wa juna sani ga ma’aikatanta da sauran masu ruwa da tsaki a fannin kare faruwar bala’o’i.
Mustapha Ahmed ya ce “babu ko shakka za a samu ambaliyar ruwa a wannan shekarar, ba mu san irin barnar da za ta yi ba amma tabbas za a samu ambaliyar ruwa.”