Gwamnatin Tarayya ta sanar da kammala duk wani tanadi na tunkarar masu tayar da kayar baya da sauran masu yunkurain wargaza Najeriya.
Gwamnatin ta ce za ta yi amfani da karfin soja wajen dakile duk wata aniya ta masu shirin kawo rudani da tayar da zaune tsaye a kasar.
- Coronavirus: Jihohi 14 da aka samu karin mutum 131 da suka kamu
- Mutumin da yake sayar wa da ’yan bindiga babura ya shiga hannu a Kano
Ministan Tsaro, Manjo-Janar Bashir Magashi (mai ritaya), ne ya sanar da hakan a taron kwana guda mai taken ‘Inganta Ayyukan Soji a Matsayin Babban Tsarin Yaki da Ta’addanci a Najeriya,’ da aka gudanar a Abuja.
Janar Magashi ya koka kan yadda Najeriya ta tsinci kanta cikin mawuyacin hali sakamakon hare-haren ta’addancin masu satar mutane da ’yan fasin daji da makamantansu.
“Muna cikin mawuyacin hali kuma muna bukatar fahimtar juna, goyon baya da hadin kai daga dukkan masu ruwa da tsaki,” inji Ministan.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Babban Hafsan Hafsoshi, Janar Lucky Irabor ya lashi takobin murkushe duk wasu masu dauke da makamai a cikin dazuka donn tabbatar da tsaro a kasar.
A cewar Ministan, Gwamnatin Tarayya, kamar kullum, ta dukufa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma bisa ga umarnin Shugaban Kasa da kuma Hafsoshin Tsaro na kawar da duk kalubale da ke addabar tsaron kasar.
Ministan ya kara da cewa, cikin shekarun da suka gabata Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da tsarin hadin gwiwa da bangarori daban-daban, inda take aiki kafada da kafada da makwabtakan kasashe a kokarinta na samar da zaman lafiya mai dorewa.