✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta tsallake rijiya da baya

Duk da kwallayen ukun da kasar Ajantina ta jefa a ragar Najeriya Super Eagles hakan bai hana ta hayewa zuwa zagaye na gaba a gasar…

Duk da kwallayen ukun da kasar Ajantina ta jefa a ragar Najeriya Super Eagles hakan bai hana ta hayewa zuwa zagaye na gaba a gasar cin kofin duniya da yanzu haka yake gudana a Brazil ba.
A shekaranjiyta Laraba ne aka fafata a tsakanin Najeriya da Ajantina a wasa karo na uku a gasar cin kofin duniya.  An tashi wasan ne Ajantina ta samu nasara da ci 3-2.
Sai dai masu sharhi a kan al’amurran kwallo sun nuna Najeriya ta yi kokari a wasan don sai da Ajantina ta yi namijin kokari kafin ta samu nasara a wasan duk kuwa da zaratan ’yan kwallon da take takama da su irin su Lionel Messi da Di Maria da Sergio Aguerro da Gago da sauransu.
Lionel Messi ne ya fara zura kwallo a ragar Najeriya a daidai minti uku yayin da dan kwallon Najeriya Ahmed Musa ya farke cin a minti na 4.  A daidai minti na 45 watau ana gab da tafiya hutun rabin lokaci ne Lionel Messi ya sake jefa kwallo ta biyu a ragar Najeriya a bugun tazara watau Free Kick.
Sai dai a minti na 47 kuma Ahmed Musa ya sake farke cin da aka yi wa Najeriya.  
A minti 50 ne kuma dan kwallon Ajantina mai suna Marcos Rojo ya sake zura kwallo ta uku a ragar Najeriya.  Haka aka cigaba da fafatawa har aka tashi Najeriya ba ta samu damar farke cin ba, haka kuma ita ma Ajantina ba ta kara ba.
Sai dai duk da wannna rashin nasara da Najeriya ta yi ta samu damar hayewa zuwa mataki na gaba saboda kasar Bosniya Herzegobina ta lallasa ta Iran da ci 3-1 a daya wasan da aka yi.
A gobe Asabar ne za a fara wasa zagaye na biyu amma Najeriya sai a Litinin ake sa ran za ta yi nata wasan.  Za ta kece raini ne da kasar Faransa yayin da Ajantina kuma ake sa ran za ta yi wasa da Suwizilan.