Kungiyar kwallon kafa ta Flying Eagles ta Najeriya, ta maza ’yan kasa da shekara 20, ta samu shiga Gasar Cin Kofin Afirka wadda za a gudanar kasar Masar a 2023.
Flying Eagles sun samu wannan nasara ne bayan da suka lallasa takwarorinsu na kasar Cote d’Ivoire ranar Talata a wasan dab da na karshe a Gasar WAFU B ta ’yan kasa da shekara 20 da ke gudana a birnin Niamey na kasar Jamhuriyar Nijar.
- Luis Suárez zai bar Atletico Madrid a karshen kakar wasanni
- Kwallo 4 a bana: Shin PSG ta yi asarar dauko Messi?
Nasarar ci 2 da 1 da Najeriya ta samu ya ba wa ’yan wasan kungiyar Flying Eagles damar zuwa wasan karshe na Gasar WAFU B, wanda za a buga ranar Asabar, da kuma tikitin shiga Gasar Cin Kofin Afirka na ’yan kasa da shekara 20 da za a yi a 2023.
Dan wasan tsakiya, Daniel Daga ne ya zura kwallo na farko a ragar abokan karawarsu bayan minti biyar da fara wasa, amma Cote d’Ivoire suka farke kafin tafiya hutun rabin lokaci.
Daga nan, babu wani bangare da ya sake samun sa’ar zura kwallo a raga har zuwa cikan lokacin wasan, lamarin da ya sanya aka yi karin lokaci don su kece raini.
Ana cikin haka ne sai dan wasan gaban Najeriya, Ibrahim Yahaya, ya zura kwallo na biyu a ragar ’yan Cote d’Ivoire a daidai minti na 111 sannan aka tashi wasa da 2 da 1.
Da wannan nasarar da Najeriya ta samu, ya tabbata za ta kara da makwabciyarta Jamhuriyar Benin a wasan karshe ranar Asabar mai zuwa.