Najeriya ta kwato Naira triliyan 3.2 na tsabar kudin da aka sace daga kasar daga shari’oi daban-daban a duniya.
Wannan bayani ya fito ne daga Babban Lauyan gwamnati kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, a ganawarsa da ’yan jarida a Fadar Shugaban Kasa a ranar Alhamis.
- An fara binciken satar N31m a Gidan Gwamnatin Katsina
- Na hannun daman Amaechi ya sauya sheka zuwa PDP
Wadannan kudadde, a cewarsa, Ma’aikatarsa ce ta jagoranci kwato su daga shari’o’i da ta wakilci Gwamnatin Tarayya a kasashen duniya a tsakanin watan Maris na 2021 da watan Mayu na 2022.
Ministan ya ce tuni aka zuba kudaden a ayyukan raya kasa a wurare daban-daban a fadin kasar nan, ciki har da ginin gada 2nd Niger, da aikin hanyar Abuja zuwa Kano, da kuma ta Legas zuwa Ibadan.
Ya ci gaba da cewa, Gwamnatin Tarayya ta samu Naira biliyan 1.82 daga sayar da takardun lamuni da kuma sayar da wasu kadarorin gwamnatin da aka kwato a watanni 18 da suka gabata.
Malami ya kara da cewa, Ma’aikatar Shari’a ta mara wa gwamnati baya wajen kulla yarjejeniyar samar da kudaden gudanar da wasu ayyukan ci gaba.
Wannan hira da ‘yan jaridu da Ministan ya halarta, shi ne kashi na 46 a cikin jerin hirarrakin da Kwamitin Yada Labarai na Fadar Shugaban kasa ke shiryawa a Abuja.