Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano ta wanke Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa daga zargin kisan kai da ake tuhumarsa.
Atoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’a na jihar, Musa Abdullahi Lawan ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai ranar Alhamis a birnin Dabo.
Lawan ya ce binciken da Ma’aikatar Shari’ar ta gudanar kan tuhumar da ake yi wa Alhassan Doguwa kan laifin kisan, ya nuna cewa ba a same shi da laifin da ake zargi ba.
Kwamishinan ya ce an samu sabani da dama cikin bayanan da aka samu daga wurin shaidu.
Ya kara da cewa, a yayin da suke gudanar da bincike sun gano cewa ma’aikatan asibiti ba su yi cikakken bincike kan mutanen da ake zargin an harba da bindiga ba, soboda haka ba a iya tabbatar da cewa an harbe su ba.
Kwamishinan ya ce an gudanar da bincike kan bindigogi da harsashai da ke hannun ’yan sandan da ke tare da dan majalisar a lokacin da rikicin ya faru.
Sai dai a bayanin nasa babu wata shaida da ta nuna cewa an yi amfani da bindigogin, kasancewar jami’an ’yan sandan sun mayar da daidai adadin harsasan da ke a hannunsu.