✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu kawo ƙarshen hukunce-hukuncen kotuna masu cin karo da juna — Ministan Shari’a

Gwamnatin Tarayya ta ƙudirin aniyar kawo ƙarshen yadda kotunan kasar ke yin hukunce-hukunce masu cin karo da juna, abin da tsawon wani lokaci ya addabi…

Gwamnatin Tarayya ta ƙudirin aniyar kawo ƙarshen yadda kotunan kasar ke yin hukunce-hukunce masu cin karo da juna, abin da tsawon wani lokaci ya addabi ɓangaren na shari’a.

Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Najeriya, Lateef Fagbemi (SAN) ne ya sanar da hakan a jiya Talata a birnin Ilori na Jihar Kwara yayin buɗe taron kwana uku na neman kawo sauye-sauye a harkokin shari’a wanda Ma’aikatar Shari’a ta Najeriya tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Tarayyar Turai suka shirya.

Mista Fagbemi ya ce sabon Alƙalin Alƙalan Najeriya a shirye yake kuma shi ma a shirye yake ya bayar da haɗin kai wajen yin wannan gyara.

Ya ƙara da cewa, shugabancin ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya ya nuna cewa lalle akwai buƙatar kawo ƙarshen wannan matsala.

Fagbemi ya ce sauye-sauyen da ake matuƙar bukata a ɓangaren shari’a suna da muhimmanci sosai ga tsari da shirye-shiryen gwamnatin yanzu na raya Najeriya.