Tsohon Ministan Shari’a kuma Atoni-Janar na Najeriya, Abubakar Malami, ya musanta rahoton cewa ya tsere daga kasar saboda gudun tuhumarsa da aikata laifuka masu nasaba da rashawa.
Wannan dai na zuwa ne bayan dakatar da Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa ta EFCC, Abdulrasheed Bawa da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a wannan makon kan zargin almundahana.
- Dalilin da na fadi zaben Shugaban Majalisar Dattawa — Abdulaziz Yari
- Ina neman afuwar Musulmai bisa furucin da na yi kan zaben Majalisar Dattawa — Kashim Shettima
Bayan dakatar da Shugaban na EFCC da kuma tsare shi da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS ta yi ne aka soma yada jita-jitar cewa Malami ya cika bujensa da iska gudun kada bincike ya biyo ta kansa.
Malami wanda ya fito daga Jihar Kebbi, ya rike kujerar Babban Lauyan Kasa tsawon shekaru takwas a wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.
Haka kuma, ya taka rawar gani wajen bai wa dakataccen Shugaban EFCC mukami, inda a wata hira ta musamman da Aminiya ya ce shi ya bayar da shawara a bai wa Bawa mukamin la’akari da cancantarsa.
Da yake karin haske, Malami ya ce ya ji dadi duk tuhumar da ake yi wa Bawa a yanzu ba saboda rashin cancanta ba ce, illa iyaka wasu dalilai na daban.
“Na yi farin ciki duk babatun da ake yi a kan Bawa ba saboda rashin cancanta ba ce ko kuma rashin kwarewa a kan makamar aiki.
“Ba a samu wanda ya bayyana shakku kan rashin cancantarsa ba a duk fadin kasar nan,” a cewar Malami a watan Maris na 2021.
Sai dai bayan dakatar da Bawa daga shugabancin Hukumar ta EFCC a ranar Laraba, lamarin ya tayar da kura kan salon riko da akalar jagoranci da Malamin ya yi.
Wata majiya ta EFCC ta shaida wa Aminiya cewa, hukumar a yanzu tana da sha’awar bincikar Malami kan sulalewar Dala biliyan 2.4 na harajin ganga miliyan 48 na danyen man fetur da aka sayar ba bisa ka’ida ba tun daga shekarar 2014 kawo yanzu.
Majiyar ta kara da cewa, akwai wasu batutuwa da tsohon Atoni-Janar din zai yi karin haske a kansu da zarar ya amsa goron gayyatar Hukumar ta EFCC.
Sai dai kuma a wata hira ta musamman da aka yi da Malami a ranar Alhamis da ta gabata, ya ce sam goron gayyatar EFCC bai karaso gare shi ba koda ta kasance akwai gayyatar a zahirance.
“Babu wata gayyata da ta riske daga EFCC ko wata hukumar yaki da rashawa a kasar.
“Kuma ina nan a Najeriya ban je ko’ina ba domin ko a gobe [Juma’ar yau] ina da daurin aure da misalin karfe 2:30 na rana a Masallacin Sheikh Isiyaka Rabi’u da ke Kano.
“Saboda haka a halin yanzu ba ni da wani shiri na barin Najeriya kuma a shirye nake na amsa goron gayyatar kowacce hukuma ta gwamnati da zarar ta iso gare ni.
“Ni dan Najeriya ne na hakika, kuma na yarda da duk wani tsari da tanadi na kasar.”