✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da na fadi zaben Shugaban Majalisar Dattawa — Abdulaziz Yari

Na yi mamaki duk da cewa babu magudi a zaben.

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Abubakar Yari, ya yi ikirarin cewa taron dangi aka yi masa, aka kayar da shi a takarar da ya yi ta neman shugabancin Majalisar Dattawa ta 10.

Sanata Abdulaziz Yari ya shaida wa BBC cewa zaben ya zo masa da mamaki saboda har zuwa lokacin da aka kai ga zaben yana da kwarin gwiwar samun nasara.

Sai dai duk da haka sanatan ya ce ya amince da shan kaye.

“Zaben majalisa, ba zabe ba ne da ake yi wa jayayya a ce ko an yi magudi, babu magudi a cikinsa, mu 109 ne kuma kowa zai zo da ra’ayinsa, da abin da hankalinsa ya ba sa ya yi, kuma sun yanke hukunci.”

Sanatan ya kuma ce da ya san ba zai ci zaben ba tun farko da bai tsaya takarar neman shugabancin Majalisar Dattawan ba.

Ya yi ikirarin cewa a ranar da su fara daukar sakamako na mutanen da ke mara masa baya sun samu adadi da zai sa su iya samu rinyaje a zaben.

Sai dai ya yi zargin cewa taron dangin da aka yi masa sannan kuma an samu wadanda suka yaudare shi wanda shi ne dalilin da ya sa ya sha kaye.

“Shugaban Kasa na ciki, Mataimakin Shugaban Kasa na ciki, haka Sakataren Gwamnati na ciki da gwamnonin, ni kadai ne sai wadannan bayin Allah.

“Ina fatan gobe idan Shugaban Kasa ya dawo a karo na biyu, zai yarda dimokuradiyya ta dauki matakinta a cikin majalisa, ya ce yana son wane amma abin adalci ga shugaba shi ne da wannan da wannan duka na kane,” in ji shi.

Sai dai duk da korafe -korafen da sanatan ya yi, ya ce dangantakar da ke tsakaninsa da shugaba Bola Tinubu ba ta sauya ba saboda ya rungumi kaddara.

“Na dauka Allah ne Ya yi, ban dauka Tinubu ne ya yi ba, Allah ne Ya yi, domin Allah ne Ya kaddara cewa zai zamo,” in ji Yari.

Aminiya ta ruwaito yadda Godswill Akpabio ya ci zaben da kuri’a 63 a kan abokin takararsa, Sanata Abdulaziz Yari wanda ya samu kuri’a 46.

Daidai lokacin da ’yan majalisar wakilai 353 suka kada kuri’unsu ga Tajuddeen Abbas, wanda ya zama Shugaban Majalisar Wakilai.

Sabbin shugabannin majalisar ta goma su ne suka samu goyon bayan jam’iyya mai mulki ta APC da kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Zaben ya kawo karshen kai ruwa da rana da takaddamar da aka shafe watanni ana yi tun lokacin da jam’iyyar APC da Shugaba Tinubu suka nuna goyon baya ga takarar Sanata Akpabio da Honarabul Tajuddeen.

Sun dai kafa hujja ne da cewa tun da Bola Ahmed Tinubu, Shugaban Kasar da Mataimakinsa, Kashim Shettima, duka Musulmai ne, ya fi dacewa a samu Kirista daga Kudancin Najeriya ya zama Shugaban Majalisar Dattawan.

Shi ne mutum na uku mafi girman mukami bisa tsarin Kundin Mulkin Najeriya.

A cewarsu, matakin zai tabbatar da daidaito wajen raba mukamai da inganta hadin kan kasar mai al’ummomi da addinai mabambanta.

Sai dai masu sukar matakin sun ce abin da APC da Shugaba Tinubu suka yi tamkar katsalandan ne cikin harkokin Majalisar Tarayya wadda tsarin mulki ya ba ta ’yancin cin gashin kanta.