✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lauyoyi mata sun nemi a kafa kotun sauraren shari’ar cin zarafi

Ƙungiyar ta ce ire-iren waɗannan kotuna za su taimaka wajen yanke hukunci cikin sauri.

Ƙungiyar Lauyoyi Mata ta Duniya (FIDA) reshen Jihar Kano, ta yi kira ga Hukumar Shari’a ta Jihar da ta samar da ƙarin kotuna waɗanda za su kula da ƙararrakin da suka shafi mata da ƙananan yara.

Wannan ya fito ne daga bakin shugabar ƙungiyar, Barista Bilkisu Ibrahim Sulaiman a lokacin bikin makon ƙungiyar da aka gudanar a Jihar Kano.

Bilkisu, ta bayyana cewa akwai buƙatar a samar da kotuna na musamamn waɗanda za sui kula da abin da ya shafi laifukan cin zarafin jinsi don a samu yanke hukunci a kan lokaci.

A cewarta a halin da ake ciki yanzu sakamakon ƙalubalen ɗage-ɗagen shari’a ya janyo iyalan waɗanda aka ci zarafi sukan haƙura su gaza bin haƙƙin ‘yan uwansu.

“Idan aka samu waɗannan kotunan batun ɗaukar shekaru ana shari’a zai zama tarihi. Duk wanda ya ci zarafi idan an kai shi wannan kotu wacce aikinta kenan, to, na tabbata idan har an daɗe a yi watanni uku zuwa shida an gama shari’a.

“Yanke hukunci a kan lokaci zai zama izna ga al’umma gaba ɗaya. Zai kuma kawo sauƙi ga faruwar cin zarafi wanda ake samun ƙaruwarsa a kullum.”

Ta kuma ƙara da cewa akwai buƙatar a samar da kotuna da za su jiɓanci lamarin ƙananan yara da mata.

“Tunda a yanzu an yi dokar kare haƙƙin yara, to, ya zama wajibi idan har ana so dokar ta yi aiki yadda ya kamata sai an samar da kotuna na musamman da za su keɓanta a gare su.”

Har ila yau ƙungiyar ta nemi Babbar Jojin da ta sa a ɗauke musu biyan duk wani kuɗi da ake bayarwa a lokacin yin shari’a duba da cewa su kansu kyauta suke yin ayyukansu.

“Kungiyarmu ba kuɗi ne da ita ba, ba ma karɓar kuɗi daga hannun waɗanda muke wa aiki. Domin mun yarda mu aikin al’umma muke yi.

“A lokuta da dama kuɗin da ake karɓa a hannunmu na shigar da ƙara ko kuma idan muna neman wasu bayanai a kotu suna yi mana yawa.

“Don haka muke neman a ɗauke mana biyan irin waɗannan kuɗaɗen a duk lokacin da muka kawo ƙara ƙarƙashin ƙungiyarmu gaban shari’a.

“Wannan abu ne da ake yi a waɗansu wurare na faɗin ƙasar nan gaba ɗaya.”

A nata jawabin, Babbar Jojin Jihar Kano, Mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ta bayyana cewa

suna nan suna aiki tuƙuru wajen ganin an samar da kotunan don tabbatar da adalci a tsakanin al’ummar jihar.

Ta kuma yi kira ga FIDA da ta ƙara zage damtse wajen gudanar da ayyukanta.

Babbar Jojin ta nemi taimakon masu ruwa da tsaki da su ruɓanya ƙoƙarinsu wajen ganin an yaƙi wannan mummunan al’amarin da ke damun al’umma.

Shi ma a nasa jawabin, Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Isah Dederi wanda ya samu wakilcin Darakta a Ma’aikatar Shari’a, Barista Hussein Hussen, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kano tana aiki tuƙuru wajen ganin mata da yara sun samu adalci a kotuna.

Ya kuma yaba wa ƙoƙarin ƙungiyar, inda ya nemi su ci gaba da zage a damtse a kan ayyukan da suke yi na zama gatan mara gata.