✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta kama hanyar gyaruwa – Remi Tinubu

Remi ta bayyana haka ne yayin taron shan ruwa da ta shirya a fadar gwamnati da ke Abuja.

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta shirya buɗa-baki a Fadar Gwamnati da ke Abuja, inda ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ƙasar nan na kan hanya gyaruwa nan ba da jimawa ba.

A yayin jawabinta, ta jaddada muhimmancin tausayi da jin-ƙai a tsakanin rayuwar ɗan adam.

Ta buƙaci kowa ya kasance mai aikata alheri tsakaninsa da Allah, ba don neman yabo ko amincewar mutane ba.

A yayin buɗa-bakin, Farfesa Azeezat Adebayo, Shugabar Sashen Nazarin Addinin Musulunci na Jami’ar Ilorin, ta bayyana cewa tausayi da jin-ƙai su ne ginshiƙai na kyakkyawar rayuwa a tsakanin al’umma.

Ta tunatar da mahalarta buɗa-bakin cewar watan Ramadan lokaci ne na koyon kyawawan ɗabi’u, kuma ana buƙatar a aikata alheri ga kowa, ba wai ga Musulmai kaɗai ba.

Daga cikin manyan baƙi da suka halarci buɗa-bakin akwai Uwargidan Tsohon Shugaban Ƙasa, Dame Patience Jonathan da matar Mataimakin Shugaban Ƙasa.

Sauran sun haɗa da matan gwamnonin jihohi, ministoci mata, matan ministoci da matan shugabannin hukumomin tsaro.