A shekaranjiya Laraba ce Kungiyar Kwallon Kafa ta Najeriya, Super Eagles ta haye zagaye na gaba bayan ta ci kasar Guinea da ci daya mai ban haushi.
Wannan sakamako ya nuna kungiyar Super Eagles ce ta farko a jerin kungiyoyin da ke fafatawa a gasar wajen hayewa mataki na gaba duk da tana da saura wasa daya.
A wasan farko Najeriya ta ci Burundi ne da ci daya mai ban haushi sannan a wasa na biyu ta sake lika wa Guinea ci daya mai ban haushi inda hakan ya sa ta hada maki 6 a wasa biyu.
Hakan ya karfafa- hasashen da wadansu ke yi na cewa Najeriya ce za ta lashe kofin a wannan karo, ganin yadda kungiyar ta fara gasar da kafar dama.
Yanzu dai Najeriya tana jiran kungiyar da za ta hadu da ita ce a zagaye na biyu idan an kammala wasannin zagayen farko a makon gobe.