✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Najeriya ta kora Kamaru gida a Gasar AFCON 2023

Najeriya za ta fafata da Angola a Kwata-Fainal; Karo na biyu ke nan da Super Eagles ke kora Kamaru a gida a matakin ’yan-16 a…

Najeriya ta tsallaka zuwa matakin Kwata-Fainal bayan da ta ba wa Kamaru taliyar karshe a Gasar cin Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) da ke gudana a Ivory Coast.

Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta casa makwabciyarta Indomitable Lions ta kasar Kamaru ne da ci 2-0 a zagayen ’yan-16 na gasar da ke gudana a birnin Abidjan.

Yanzu dai Najeriya za ta fafata da Angola, wadda ta kora Namibia gida a gasar.

Dan wasan Najeriya Ademola Lukman ne ya kora Kamaru inda da ci biyu, wadanda har aka tashi babu wanda Kamaru ta farke.

Bayan mintoci 9 da fara wasan ne Ademola Lukman ya zura kwallon farko a ragar golan Kamaru, Fabric Ondoa, wanda aka fi sani da Onana.

A minti na 90 kuma Lukman ya samu nasarar kara nana wa Onana kwallo ta biyu, ya kora su gida.

Sau biyu ke nan da Najeriya ta kora Kamaru a gida a matakin ’yan-16 a Gasar AFCON bayan na 2019, wanda ta ci su 3-2 a kasar Masar.

Super Eagles ta danne Kamaru da wasan da suka fafata a filin wasan da Kamarun ta fara cin kofin AFCON wanda a lokacin ta doke Najeriya a wasan karshe a 1984.

A wasan ne a karo farko a gasar Kamaru ta sanya Kyaftin dinta da ya sha fama da rauni, Vincent Aboubakar, wanda shi ne dan wasan da ya fi zura kwallo a gasar 2021. Amma duk da haka, aka ta shi 2-0, ba tare da Kamaru ta girgiza ragar Najeriya ba.

Kafin yanzu sau uku Kamaru na koro Najeriya gida daga gasar AFCON 2023.

A wannan karon, da alama dai kocin Kamaru, Rigobert Song, zai sha caccaka a gida kan cire su da aka yi a wannan karon, musamman ganin cewa a Gasar Cin Kofin Duniya na 2022 ba su su tsallake zagayen farko ba.

Za bi dai na hannun shugaban kungiyar kwallon kafan Kamaru, Samuel Eto’o, na sallamar Son ko barin tsohon abokin wasan nasa ya ci gaba da aiki.