✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hankalin jama’a na daɗa tashi saboda tsadar kayan abinci

Yanzu haka ana sayar da buhun gero mai nauyin kilo 100 a Kano a kan Naira 51,000.

Karuwar tsadar kayan abinci na dada jefa jama’a a cikin tashin hankali, inda suke ci gaba da tattauna batun a sassan kasar nan.

Aminiya ta samu ta samu bayani a Jihar Kano cewa, farashin shinkafa, masara, gero da sauran kayan amfanin gona na tashi a kusan kullum, al’amarin da jama’a ke bayyana shi da abin damuwa kuma mai tattare da hadari ga rayuwar dan Adam.

Alkaluma sun nuna cewa hauhawar farashin kayan masarufi ya kai kimanin kashi 30 cikin 100, wanda shi ne mafi muni a ’yan shekarun nan.

Bincike ya nuna cewa yanzu haka ana sayar da buhun gero mai nauyin kilo 100 a Kano a kan Naira 51,000, buhun shinkafa, Naira 92,000 sai masara Naira 44,000.

Wannan matsala ta shafi kusan dukkan kayayyakin amfanin gona, wanda hakan wata barazana ce ta fuskar wadatar abinci.

Wani mai sayar da hatsi a Kasuwar Dawanau, Alhaji Uba Abdullahi Bello, ya ce yawan fitar da kayayyakin amfanin gona zuwa kasashe makwabta da manyan kamfanonin ke yi ne ya janyo tashin farashin kayayyakin abincin, musamman a Jihar Kano.

Ya ce “Ku sani ana fitar da kayayyakin mabincinmu zuwa kasashen waje, ko dai bisa ka’ida ko ba bisa ka’ida ba.

“A yanzu kayayyakin abincinmu sun zama abin rubibi a kai, ba don komai ba, sai domin yadda mutanenmu ke tururuwar kai kayan don samun kudaden waje wadanda idan ka canza su manyan kudade ne.

“Har ila yau, akwai kuma yawaitar neman albarkatun kasa da kamfanonin sarrafa kayayyaki ke yi.

“A bayyane yake cewa akwai gasa sosai a tsakanin masu bukatar kayan da kuma masu neman albarkatun kasa daga wadannan manyan kamfanoni.

“Wanda hakan ne ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki saboda yawaitar masu bukata,” in ji shi.

Wasu magidanta a Jihar Kano sun nuna fargabar samun karancin abinci sakamakon tsadarsa. Malam Bashir Idris, wani karamin ma’aikaci ne ya ce akasarin kayan abinci sun gagari mai karamin karfi, inda ya ce a yanzu sayen kwanon wake ko shinkafa na neman fin karfin talaka, inda ya kara da cewa mutane da dama sun koma sayen gwangwani daya ko biyu a dafa.

“A halin da ake ciki inda mafi karancin albashi ya kasance Naira dubu 30 kuma ana sayar da tiyar shinkafa a kan Naira dubu 2,300, yaya kake tunanin rayuwa za ta kasance?

“Yanzu haka ana sayar da tiyar sukari a kan Naira 4,000 yayin da tiyar masara ta kai Naira 1,200.

“Mutum zai zubar da hawaye idan ya ga yadda al’umma ke fama a cikin irin wannan hali.

“Maganar gaskiya ita ce Nijeriya da al’ummarta na cikin mummunan hali, kuma akwai bukatar gwamnati ta shigo cikin lamarin,” in ji shi.

Bayan hauhawar farashin shinkafa ’yar gida da sauran kayayyakin amfanin gona a Jihar Kano, Kungiyar Sasakawa Africa Association (SAA), wacce ta kasance abokiyar hadin gwiwar Hukumar Bunkasa Aikin Gona ta Jihar Kano (KSADP), wanda Bankin ci gaban Musulunci (IsDB), ke daukar nauyin gudanar da ayyukanta da Asusun Inganta Rayuwa da Ci-gabanta (LLF) da kuma Gwamnatin Jihar Kano, sun kaddamar da ayyukan da za su tabbatar da an samu yawan noman shinkafa don samun sauki ga jama’a.

Da yake zantawa da Aminiya, Mataimakin Daraktan Kungiyar SAA ta Kasa, Dokta Abdulhamid Gambo, ya ce kungiyar ta shafe sama da shekara 34 a Jihar Kano tana tallafa wa manoma, ba wai ga masu noman shinkafa kadai ba har da sauran kayayyakin amfanin gona.

Ya ce, yanayin hauhawar farashin kayayyakin amfanin gona yana da nasaba da yanayin da duniya ke fuskanta kan matsalar tattalin arziki.

A cewarsa, Kungiyar SAA ta fara horar da manoma da kuma bai wa manoman fasahohin da ake bukata don noma domin tabbatar da samun amfanin gona mai kyau da kuma karuwar kudaden shiga.

Ya kara da cewa ta haka ne aka samu yawaitar amfanin gona.

“A halin yanzu muna inganta ayyukan noma ta yadda muka koya wa manoma dabarun da ake amfani da su da kuma samar musu da iri mai kyau, baya ga horar da su dabarun noman zamani da sauransu.

“Mun samu karuwar noman shinkafa daga tan 2 a kowace kadada zuwa kusan tan 5. Wannan wani kyakkyawan ci gaba ne na magance matsalar noman shinkafa,” in ji shi.

Hakazalika, jami’in da ke kula da Hukumar Bunkasa Aikin Gona ta Jihar Kano (KSADP), Malam Abdulrasheed Hamisu Kofar Mata, ya ce a karkashin shirin an samar da hanyoyin da manoma za su iya amfani da su, tare da koyar da su dabarun farfado da ayyukan noma.

Ya ce aikin ba wai ya tsaya a kan harkar noma kadai ba ne, har da inganta noman shinkafar gida ta hanyar horar da mata sama da 2,500 kan yadda za su gyara shinkafa ta hanyar amfani da tsarin kungiyarsu.

“Mun kuma samar da cibiyoyin sarrafa shinkafa sama da 30 a kananan hukumomin jihar 44 domin bunkasa sana’ar casar shinkafar, tare da kara habaka ayyukan da muke yi kan noman shinkafa.

“Ta hakan ne muke fata za mu bayar da gudunmawa wajen rage farashin irin shinkafa da kuma ita kanta shinkafar gidan a Jihar Kano,” inji shi.

Yayin da al’ummar Musulmi ke shirin tarbar watan azumin Ramadan nan da wani lokaci, jama’a da dama suna nuna damuwarsu a kan yadda farashin kayayyaki ke kara hauhawa a kullum.