Sarkin Benin, Oba Ewuare II, ya bukaci a koma mulkin wa’adi daya na shekara shida ga masu rike da kujerun siyasa musamman gwamnoni da shugaban kasa.
Babban Basaraken mai daraja ta daya ya yi kiran ne a fadarsa, yayin karbar bakuncin tawagar manyan jami’an Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) wanda shugabanta, Farfesa Mahmoud Yakubu ya jagoranta.
Sarki Ewuare ya yi kira da sauya salon tsarin shugabanci a kasar wanda a cewarsa, baya ga rage kudin da za a fitar, zai kuma taimaka wajen rage tashin-tashinar da ke aukuwa ta hankoron wa’adi na biyu.
Yana mai cewa, “ban kasance kwararre a fagen siyasa ba, amma a iya hangen nesa da na yi, idan aka bi wannan shawara za ta taka rawar gani wajen magance yanayin da aka fuskanta a lokutan baya”.
Ya nemi ’yan siyasa da su yi koyi da tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, wanda saboda zaman lafiya ya ci gaba da wanzuwa a kasar ya amince da sakamakon zaben da a yanzu Shugaba Muhammadu Buhari yake cin gajiyarsa.
Yayin kira ga ’yan siyasa da su raba kawunansu da tayar da tarzoma, ya ce neman wani abin duniya bai kai kwatankwacin darajar ran mutum daya ba.
Ya ba da tabbacin cewa zai aike da goron gayyata ga dukkannin ’yan takarar Gwamnan Jihar Edo da za su fafata a zaben da za a gudanar, domin su rattaba hannu a kan yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya.
A nasa jawaban, Shugaban INEC Farfesa Yakubu, ya ce sun ziyarci fadar sarkin ne domin neman tabarrakinsa a kan zaben jihar da za a gudanar a watan Satumba.