Wakilan wasan damben boksin da suke wakiltar Najeriya a Gasar Wasanni ta Afirka karo na 11 da ake gudanarwa a Kongo Brazzabille sun zo na biyu a teburin gasar damben a bayan kasar Aljeriya.
Ayarin Najeriyan ya lashe lambobin zinare hudu da azurfa biyu, yayin da Aljeriya ta lashe lambobin zinare biyar da azurfa daya.
Najeriya ta kara cirawa sama a damben boksin din idan aka kwatanta da rawar da ta taka a wasan baya da aka gudanar a Maputo kasar Mozambikue a shekarar 2011, inda Najeriya ta kare a ta shida ta hanyar lashe lambobin azurfa uku da tagulla daya.
dan damben boksin na Najeriya, Olufemi Oyeleye ya doke Nsango Njikam na Kamaru inda ya samu lambar zinare a ajin masu matsakaicin nauyi.
Sai Efe Ajagba ya doke Keddy Angnes a ajin masu nauyi na Super Heabyweight, ya tashi da lambar zinare. A bangaren mata, Edith Ogu-Ogoke ta doke Rana Abdelhamid ta Masar a ajin matsakaicin nauyi, yayin da Kehinde Obareh ta make Hilimi Khouloud ta Tunsiya a aji marar nauyi.
Sai Caroline Linus wadda ta samu lambar azurfa a aji mai nauyin kilo (48-5kg), yayin da Efe Apochi ya lashe azurfa a aji matsakaicin nauyi na maza.
Najeriya ta ci lambobin zinare hudu a damben boksin
Wakilan wasan damben boksin da suke wakiltar Najeriya a Gasar Wasanni ta Afirka karo na 11 da ake gudanarwa a Kongo Brazzabille sun zo na…