✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta bukaci Facebook ya rufe shafin IPOB

Najeriya za razin IPOB da zargin yada lakaman tsana da kuma tunzura jama'a su yi tashin hankali.

Gwamnatin Najeriya ta bukaci Facebook da sauran kafofin sada zumunta su rufe shafukan kungiyar ta’addanci ta IPOB saboda yada kalaman tsana da tunzura jama’a.

Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, shi ne ya yi kiran kamar yadda kakakinsa, Segun Adeyemi, ya sanar ranar Talata a Abuja.

Lai Mohammed ya ce: “Na kira zaman nana ne kan matsalar karuwar yadda masu neman ballewa daga Najeriya da masu saboda doka, suke amfani da Facebook, musamman daga kasashen waje, suna tayar da rikici da yada tsana a tsakanin ’yan Najeriya.

“Su suka san dalilin da suka fi son amfani da Facebook; kuma babban abin da suke yi shi ne yada labaran karya da kalaman tsana da na tunzura jama’a.

“Suna amfani da Facebook domin isa ga dubban mabiyansu, tare da ‘Tagging’ din masu adawa da tashin hankalinsu a matsayin ‘’yan hana ruwa gudu’ da ya kamata a kai wa hari a kashe.

“Da harshen Turancin Ingilishi da kuma harsunansu na iyaye da kakanni, yadda suka ga dama, suke yada wadannan abubuwa.

“Yadda suke yada kalaman batanci da tunzura jama’a ya sa an kashe mutane, an kai hare-hare tare da lalata dukiyar jama’a da na gwamnati; inda suka fi kai wadannan hare-hare kan jami’an tsaro da cibiyoyin gwamnati.

“Jami’anmu na lura da kafofin sada zumunta na sanya ido kan abubuwan da masu neman ballewa daga Najeriya da masu yada kalaman tsana da tunzura da labaran karya da ma ayyukansu a Facebook.

“Sun kuma kai kara, amma amsar da kamfanin ke bayarwa kawai, shi ne cewa ya samu korafin kuma yana nazari a kai.

“Yawanci babu abin da kamfanin ke yi kai; Gaskiyar magana ita ce babu abin a zo a gabin da kafar ke yi game da wadannan abubuwa.