Rundunar Sojin Najeriya, ta musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewar an kafa sansanin sojojin Faransa a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Kaftin Reuben Kovangiya, ya fitar.
- ’Yar Arewa ta zama mace ta farko mai tuƙa jirgin Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya
- ’Yan Yahoo 159 ’yan kasar waje da ’yan Nijeriya 599 sun shiga hannun EFCC a rana guda
Ya bayyana cewa babu gaskiya a zancen, kuma bidiyon da ake yaɗawa ba shi da alaƙa da sojojin Faransa.
Kaftin Kovangiya, ya yi ƙarin haske cewa jami’in da aka gani a bidiyon ba sojan Faransa ba ne.
Ya ce mamba ne na ƙungiyar bayar da shawara kan harkokin soji ta Birtaniya (BMATT), wadda ke aiki tare da sojojin Najeriya wajen yaƙi da ‘yan ta’adda.
Ya yi gargaɗi kan yaɗa jita-jita da labaran ƙarya a shafukan sada zumunta.
Sojojin Najeriya sun jaddada cewa suna ci gaba da haɗa kai da abokan hulɗarsu na ƙasa da ƙasa domin magance matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar.