Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta ce za ta nemi hukumomin kasar Saudiyya su dawo mata da kudin abincin alhazanta saboda ta ba su gurbataccen abincin.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Laraba, ta ce Shugabanta na kasa, Zikrullah Kunle Hassan ne ya bayyana haka a Muna, da ke Saudiyya, lokacin da ziyarci tantunan alhazai na jihohi.
- ‘Yadda muke damfarar ’yan kasuwa da ‘alert’ na bogi’
- An kama daya daga cikin tserarrun fursunonin kurkukun Kuje a Ogun
Ya ce tuni suka rubuta wasika zuwa ga hukumomin Saudiyya da suka kamata kan yanayin abincin da aka ba alhazan wanda suka yi ta korafi a kan ingancinsa.
Rashin abinci mai kyau dai na daya daga cikin tarin matsalolin da suka yi wa alhazan Najeriya katutu yayin aiki Hajjin na bana.
A cewar Zikrullah, an sami matsalar abincin a Muna ne saboda hukumomin Saudiyya ne suka karbe ragamar ciyar da alhazan, sabanin yadda ake yi a baya.
Shugaban ya kuma yaba wa alhazan kan hakuri da fahimtar da suka nuna duk da tarin kalubalen, yana mai cewa Aikin Hajji dama ya gaji jarabawa iri-iri.
Daga nan sai ya hore su da su ci gaba da kasancewa jakadun Najeriya na gari, a ragowar lokacin da ya rage musu a can.