Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya ce Najeriya na cikin jerin kasashen da suka fi fama da matsalar karancin abinci a fadin duniya.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wani sabon rahoto mai lakabin ‘Article IV’ da asusun ya fitar ranar Laraba, bayan tattaunawa da hukumomin Najeriya.
A cewar IMF, “Birbishin yakin Rasha da Ukraine, wanda ya haifar da tashin farashin kayan abinci, ya kuma kara ta’azzara halin da annobar COVID-19 ta jefa kasar, musamman talakawan cikinta, kuma Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka fi shafuwa.”
Daga nan sai asusun ya sake jaddada bukatar inganta harkar noma domin samar da aikin yi da bunkasa samar da abinci a kasar.
Kazalika, rahoton na IMF ya ce harkar hakar danyen mai ma na fama da matsalar hakowa da faduwar farashi, kamar yadda harkar noma ke fuskantar koma-baya mai alaka da sauyin yanayi.
Daga nan sai IMF ya shawarci hukumomin Najeriya da su tabbatar sun cire tallafin mai gaba daya nan da tsakiyar wannan shekarar sannan su bunkasa shirye-shiryen tallafa wa masu karamin karfi.
Sai dai duk da yaba wa Najeriya kan yunkurinta na fadada hanyoyin samar da kudaden shigarta, IMF ya ce kasar ta gaza cin gajiyar tashin gwauron zabon da farashin danyen mai ya yi a kasuwar duniya yadda ya kamata.