Wani rahoto da aka fitar ya nuna Najeriya ce take a matsayi na biyar daga cikin kasashen da ’yan kwallonsu suke tururuwa sassan duniya don bugawa kulob-kulob.
Brazil ce ta farko sai Ajantina ta biyu sai Faransa ta uku sai Serbiya ta hudu sannan sai Najeriya a mataki na biyar.
Kamar yadda rahoton da wata cibiya da ke nazarin yadda ’yan kwallo ke canza sheka mai suna GES Football Obserbatory ta nuna, Najeriya ce ta fi yawan ’yan kwallon da ke wasa a ketare a duk fadin Afirka. Rahoton ya ce kawo yanzu Najeriya tana da ’yan kwallon da ke wasa a sassan duniya da yawansu ya kai 596.
Sauran kasashen Afirka da ke biye da Najeriya da rahoton ya bayyana su sun hada da Senegal da take matsayi na 10 da yawan ’yan kwallo 377 sai Kwaddebuwa da take a matsayi na 11 mai yawan ’yan kwallo 370 sai Kamaru ta 12 da take da ’yan kwallo 365.
Rahoton ya nuna yawan ’yan kwallo dubu 18 da 660 ne dai suke yin wasa a sassan duniya daga kasashe 194 a binciken da cibiyar GES ta gudanar.
Brazil ce take sahun farko bayan ’yan kwallonta su kimanin dubu 1 da 784 sun kwarara sassan duniya don yin kwallo. Ajantina kuma tana da ’yan kwallon da yawansu ya kai 929 a sassan duniya sai Faransa mai yawan ’yan kwallo 758.
Rahoton ya ce wadannan kasashe uku sun dauki kashi 20 bisa 100 na yawan ’yan kwallon da ke tafiya sassan duniya don yin kwallo.
Najeriya ce ta biyar a jerin kasashen da ’yan kwallonsu suka fi fita kasashen ketare
Wani rahoto da aka fitar ya nuna Najeriya ce take a matsayi na biyar daga cikin kasashen da ’yan kwallonsu suke tururuwa sassan duniya don…