Jerin kasashen da suka fi fama da ta’addanci na (Global Terrorism Inded -GTI)na shekarar 2018, ya nuna cewar Najeriya ce kasa ta uku da ta fi fama da matsalar hare-haren ta’addanci a duniya. Rahoton Hukumar Kididdiga Ayyukan Ta’addancin ya ce, Najeriya na fuskatar wannan matsala ce sanadiyar hare-haren ’yan ta’addan kungiyar Boko Haram, da rikice-rikicen makiyaya da manoma, kamar yadda jaridar Premium Times ta wallafa.
A rahoton shekarar 2014 an ayyana Najeriya a mataki na hudu, kuma Najeriya ta kasance cikin matsanancin hali da ya mayar da ita zuwa mataki na uku, inji hukumar.
Rahoton wanda aka fitar a shekaranjiya Laraba, ya bayyana Iraki da ke Gabas ta Tsakiya, a matsayin kasa ta farko, matakin da take kai tun daga shekarar 2014.
Sai kasar Afghanistan ke biye mata a matsayin kasa ta biyu.
Kasar Syria ce kasa ta hudu, sannan kasar Pakistan ce ta biyar a cikin kasashen da suka fi fama da ta’addanci.
Ragowar kasashen da suka fito cikin kasashe 10 da suka fi haduwa da hare-haren ’yan ta’adda tun daga shekarar 2017, sun hada da kasar Somaliya ta shida, sai kasar Yemen ta bakwai, sai Masar ta tara, sannan ta goma ita ce kasar Philippines.
Sai dai abin ban sha’awa shi ne, an samu raguwar yawaitar mace-mace a sanadiyyar hare-haren ’yan ta’adda a Najeriya a shekarar 2017, kamar sauran shekaru da suka gabata a cewar rahoton.