✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ba ta fuskantar barazanar karancin abinci, Inji Audu Ogbeh

Duk da annobar tsutsa a gonaki, Ministan Noma da Raya Karkara, Cif Audu Ogbeh ya ce babu barazanar karancin abinci a Najeriya. Ogbeh ya yi…

Duk da annobar tsutsa a gonaki, Ministan Noma da Raya Karkara, Cif Audu Ogbeh ya ce babu barazanar karancin abinci a Najeriya.
Ogbeh ya yi furucin ne a yau a taron koyon dabarun yadda kasashen Afirka ta yamma za su tunkari annobar tsutsa a kasashensu.
Kungiyar Samar da Abinci da Bunkasa Albarkatun Noma ta (FAQ) ta shirya taron wanda ya tara masu ruwa da tsaki na kasashen Afirka ta yamma don a samar da mafita ga annobar kwarin.
Ya bayyana cewa duk da annobar tsutsar da ta barke a jihohi da dama kasar ba ta fuskantar wata barazanar karancin abinci sai dai tsadar abincin a kasuwa.