More Podcasts
Duk wanda ya shekara arba’in zuwa sama ya san irin tarbiyyar da ya samu daga wurin iyayensa a da, da irin mu’amalar da ke tsakaninsa da iyaye da kuma irin shaƙuwar da ke tsakanin ’ya’ya da iyaye.
A yanzu kuwa, abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincaɓe suka yi wa iyaye yawa.
Ɗaya daga cikin manyan sauyin da aka samu shi ne aikin gwamnati ko aikin wata da iyaye mata suke yi a wannan zamani wanda a wasu lokuta ke barazana ga irin kulawar da ’ya’ya suke samu.
- NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ‘Yan Gwagwarmaya Ke Shiga Tasku A Najeriya?
- DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A Najeriya
Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne kan irin ƙalubalen da iyaye ke fuskanta a wannan zamani wajen tarbiyyar ’ya’yansu.
Domin sauke shirin, latsa nan