Ana fargabar cewa gobara ta yi ajalin wata uwa da ’ya’yanta biyu a yankin Onipakala da ke Ƙaramar Hukumar Ondo West a Jihar Ondo.
Bayanai sun ce musibar ta auku ne da tsakar daren Lahadi yayin da jama’a ke sharar barci, lamarin da ya jefa makwabta cikin zullumi.
- Saudiyya ta bai wa Kano da Abuja tallafin dabino albarkacin watan Ramadana
- Mutum biyu sun shiga hannu kan yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe a Yobe
Aminiya ta ruwaito cewa, zuwa wayewar gari Litinin, matar da ’ya’yanta —Bukola da Ifeoluwa— sun ƙone ƙurmus a sakamakon gobarar.
Wani maƙwabcinsu da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce tun tsakar dare gobarar ta tashi amma ana ji ana gani ta rutsa da mutanen uku saboda babu wata hanya da za a iya ceto rayuwarsu.
Shugaban ƙungiyar masu gidajen haya, Mista Adegbulu, ya bayyana takaicin yadda ’yan kwana-kwana suka gaza kawo ɗauki a sanadiyyar rashin ruwan kashe gobara da suka yi iƙirarin ya yanke musu.
“Mun kira su a wayar tarho a lokacin da gobarar ta tashi, amma sai suka shaida mana cewa ruwa da sauran sunadaran kashe gobarar ya yanke musu.
“Kuma nan da nan ma jami’in ya kashe wayarsa,” in ji shi.
Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin ofishin Hukumar Kashe Gobara da ke Akure, amma lamarin ya ci har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Mazauna da dama sun bayyana alhini kan aukuwar lamarin da kawo yanzu ba a kai ga gano musabbabinsa ba.
Funmilayo Odunlami-Omisanya, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ta bayyana cewa tuni an miƙa gawarwakin mamatan zuwa Babban Asibitin Ondo.
Wannan iftila’i na zuwa ne ƙasa da mako guda da wasu ƙananan yara biyu ’yan gida ɗaya suka riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar wata gobara da ta tashi a wani gida a birnin Akure.