✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAJERIYA A YAU: ‘’Yar uwata ta sume saboda rashin samun zuwa Hajji’

Wasu maniyyatan sun biya kudin tafiya Hajji tun a shekarar 2020 amma ba su samu zuwa ba

Dubban maniyata a Najeriya sun yi jiran gawon shanu, duk kuwa da cewa sun cika duk ka’idojin da ya kamata.

Wasu maniyyatan sun biya kudin tafiya Hajji tun a shekarar 2020, amma hakar su ba ta cimma ruwa ba, duk da karin lokaci sau biyu Saudiyya ta yi wa Hukumar Aikin Hajji na kwashe alhazai.

Shirin Najeriya a Yau ya tattauna da wadanda abin ya shafa da masu ruwa da tsaki a harkar jigilar maniyata.