More Podcasts
Domin sauke Shirin latsa nan.
’Yan Najeriya na yi wa kasarsu kirari da cewa ‘kasa daya, al’umma daya’.
Amma ’yan Arewacin kasar mazauna yankin Kudu sun koka bisa yadda suka yi zargin an mayar da su abin kashewa da kuma tsangwama a yankin da suke zama.
- Najeriya A Yau: Dalilin Da Masu Shiga Tsakanin Hukumomi Da ’Yan Ta’adda Ke Samun Matsala
- DAGA LARABA: Yadda Abincin Dan Adam Ke Iya Zama Guba
Shin ina ’yancin da tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowane dan kasar na zama a duk inda yake so a bisa doka, ba tare da an cutar da shi ko an nuna masa wariya ba?
Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da wasu ’yan Arewa mazauna Jihar Anambra kan yadda suke rayuwa a can.