✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya A Yau: Yadda Tinubu da Dattawan Arewa Suka Yamutsa Hazo Kan Zaben 2023

Dalilan Tinubu na bayyana aniyar takararsa a Fadar Shugaban Kasa da kuma wanda Kungiyar Dattawan Arewa ke son ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben…

More Podcasts

Domin sauke shirin latsa nan

Bayyana aniyar takarar shugaban kasa a zaben 2023 da Bola Ahmed Tinubu ya yi a Fadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta tayar da kura a fagen siyasar Najeriya.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya zakulo dalilan Tinubu na bayyana maganar takarar tasa a Fadar Shugaban Kasa da kuma matsayar Kungiyar Dattawan Arewa dangane da wanda suke son ya yi takarar shugaban kasa a zaben 2023.