✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAJERIYA A YAU: “Tabbas Muna Biyan Ma’aikatan Borno Albashin N7,000”

Wani ma'aikaci ya ce ya shafe shekara 20 yana aiki amma ana biyanshi dubu tara a wata.

More Podcasts

Shafukan sada zumunta sun girgiza bayan da wani labari ya bayyana game da yanayin walwalar ma’aikata da albashinsu a Jihar Borno.

Ma’aikata da dama sun yi ta yada hotunan sakon albashinsu na N7,000; wasu N8,000 ko N13,000 ko N15,000 ga ma’aikatan lafiya.

Shirin Najeriya a Yau ya gano gaskiyar abin da ya sa gwamnatin Borno ke biyan irin wannan albashi da bai taka kara ya karya ba.

Domin sauke cikakken shirin, latsa nan