✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAJERIYA A YAU: Wane Ne Zai Zamo Sabon Shugaban Jam’iyyar APC?

An shiga ruɗani a jam’iyar APC bayan saukar Sanata Abdullahi Adamu daga shugabancin jam’iyar, duk da yake bai wuce shekara guda a muƙamin nasa ba,…

More Podcasts

An shiga ruɗani a jam’iyar APC bayan saukar Sanata Abdullahi Adamu daga shugabancin jam’iyar, duk da yake bai wuce shekara guda a muƙamin nasa ba, inda wasu rahotanni ke cewa rashin jituwa tsakanin shugaban na APC da Bola Tinubu ne ya tursasa masa sauka daga kujerar.

Dama wasu sun dade suna jiran ganin yadda za ta kaya tsakanin shugaban kasar da Shugaban jam’iyyar APC mai murabus Abdullahi Adamu bayan zaɓe.

Shirin Najeriya a Yau, ya duba makomar jamiyar APCn da ƙaluabalen da ke gabanta game da mataki na gaba da za ta ɗauka.

Domin sauraren shirin ko saukewa kaitsaye, a latsa nan